Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta gina wa Fulani makiyaya matsugunan filayen kiwo a jihohi domin a magance yawaitar tashe-tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma.
Ministan Gona Aujdu Ogbeh ne ya bayyana haka, jiya Litinin Abuja, yayin da ya ke bude taron Sanin Makamar Aiki da ma’aikatar sa ta shirya wa ma’aikatan ta tare da sabbin masu mukaman siyasa da aka nada a ma’aikatar.
Ya ci gaba da cewa a cikin shekarar nan ta 2018, ma’aikatar sa za ta tsunduna sosai wajen kiwon shanu ta hanyar yi wa matan shanu allura wadda za a rika dura musu maniyyin bajimin sa, kuma su haihu ba tare da an yi musu Barbara ba.
“Mu na dukkan kokarin da za mu gamun magance rikice-rikicen makiyaya da manoma.
“Na san wasu za su ce ai fita yawon kiwon dabbobi abu ne da su ka gada na al’ada, to amma duk al’adar da ke haddasa kashe-kashen rayukan jama’a, tilas ne a sake yin duba kan ita wannan al’adar.
“Jihohi 16 sun ba mu filayen da za mu yi aikin kafa wuraren kiwon, sai dai kuma shirin ba mai arha ba ne, amma shi Shugaban Kasa ya shaida min cewa idan mu ka nemi taimakon sa, to zai ba mu fiye ma da abin da mu ka ware a kasafin da muke yin a abin da aikin zai ci.
“Su ma makiyayan da mu ka samu zantawa da su, abin da su ke ce mana shi ne, matukar za su rika samun ruwa da ciyawa a wuri daya, ” to ba mu da wani dalilin da zai sa mu rika yin kaura daga nan zuwa can.” Inji Audu Ogbeh.