Dan kunar bakin wake ya kashe mahaifin sa da wasu a masallaci

0

Wani dan kunar bakin wake ya kashe mahaifin sa da wasu masallata a daidai suna sallar asuba a garin Gamborun Ngala.

Matashin dai ya dade da yin hannun riga da mahaifin sa da sauran ‘yan uwansa inda ya koma da zama dajin Sambisa.

Jiya ya shigo unguwar daure da jigidar bamabamai, daidai ana sallar asuba, wanda mahaifin sa na tare da masallatan ya ko ta da bam din a masallacin.

Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukan su a harin inda wasu 10 suka sami raunuka a jikkunan sa.

Kwamandan Rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ ya ce bayan haka sun dakile wani harin kafin a yi shi a garin Rann.

Share.

game da Author