Galan daya na fetur ya kai N2,500 a Maiduguri

0

Har yau a jihar Barno ba a san ranar kawo karshen matsanancin tsada da wahalar samun fetur ba, yayin da tsanani ya sa ana saida galan daya naira 2,500.

Har zuwa jiya Talata akasarin gidajen mai a Maiduguri a kulle su ke, saboda babu mai, yayin da daruruwan motoci ke kan layin zaman-tsammanin samu a wani gidan mai daya da ke saida mai a farashin gwamnati, wato NNPC Mega Station, na Maiduguri.

Sauran gidajen mai kalilan da ke bude, su ne saida kowace lita ce akan naira N250.

Share.

game da Author