Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa darasin da ya koya a lokacin da ya ke mulkin soja ne ya sa a yanzu ba ya gaggawar gudanar da kowane aiki na tafiyar da mulkin sa.
Ya ce a yanzu ya gwammace ya tsaya tsaf ya yi nazarin duk wasu bukatu ko lamurran ayyukan da aka kawo kan teburin sa, kafin ya amince da su tukunna.
Buhari ya ce ya yi tunanin bayan yin ritaya daga soja, daga baya kuma ya dawo kan mulki, don haka a rayuwar sa, babu daren da jemage bai gani ba, ya ce dalili kenan shi ba ya yin gaggawa wajen aiwatar da komai a sha’anin mulkin sa.
Wannan furuci ya furta shi ne a lokacin da ya ke ganawa da manya da magoya bayan ‘yan jam’iyyar sa ranar Alhamis da rana, shirin da gidan talbijin na Channels ya nuna kai tsaye, a Abuja.
“Na gayyato ku ne domin ku zo, mu ci kuma mu sha tare da ni, kuma a zaman nan da na ke yi, ina tabbatar muku da cewa ina sane da dukkan matsalolin da ke damun kasar nan. Amma a ko da yaushe ina sara kuma ina duban bakin gatari” Haka Buhari ya bayyana.
A ko da yaushe dai Buhari kan dauki tsawon lokaci kafin ya aiwatar da wasu ayyuka ko da kuwa na fatar baki ne, ciki har abubuwan da ‘yan kasa ke korafi idan su ka ga an bar su a duhu.
Buhari yi jinkirin nada ministoci har tsawon watanni shida, abin da masu lura da tattalin arzki suka ce wannan ne ya jefa kasar nan cikin matsanancin kuncin da aka shiga a 2015.
Sai dai wani mai nazarin siyasar kasar nan, mai suna Eluma Asogwa, ya bayyana cewa kalaman Buhari abin dariya ne idan aka yi la’akari da abubuwan da ya gudanar cikin shekaru biyu da suka gabata.