‘Yan adawa ba su isa su hana ni shiga Kano ba – Kwankwaso

0

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso, ya karyata zargin cewa wai ya soke shirin da ya yi na shiga Kano tare da rundunar magoya bayan sa a ranar 30 Ga Janairu, 2018, wai saboda dalili na rashin lafiya.

Tun tuni dai ake ta tunanin cewa ziyarar za ta iya haddasa mummunan rikici tsakanin magoya bayan sa da na gwamna Abdullahi Ganduje.

Cikin makon da ya gabata sai da ‘yan sanda suka kama Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Abdullahi Abbas, a bisa dalilin wani furuci da ya yi cewa idan Kwankwaso da magoya bayan sa sun shiga Kano, a yi musu jifar shaidan.

Kakakin yada labaran Kwankwaso, Binta Barbiu, ta ce Kwankwaso zai je Kano tabbas, kuma ba a canja ranar da aka aza cewa zai je ba.

Kwankwaso ya ce Ganduje ne ya kitsa karyar cewa wai ba shi da lafiya. Don haka adawa ba ta isa ya hana shi shiga Kano shi da rundunar sa ba.

Share.

game da Author