Neman Duniya ya rudi maza a Jigawa aikata fyade ga kananan yara babu kakkautawa

0

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa Abdu Jinjiri ya bayyana cewa abin damuwa ne gare su da kuma gwamnatin jihar yadda fyade ya zama ruwan dare a jihar.

Ya ce koke-koken da suke samu na aikata fyade a shekaran 2017 ya fi na shekaran 2016.

“Bincike ya nuna cewa dattijai masu shekaru 50 zuwa 60 ne aka fi samu da aikata wannan mummunar laifi a jihar.”

Karuwar hakan na da nasaba da canfin da ake yi na wai idan mutum ya sadu da ‘yar karamar yarinya zai yi kudi, sannan yana Kara karfin gaban namiji Kuma yana warkar da cutar Kanjamau.

A ganawa da tayi da PREMIUM TIMES kwamishinan harkokin mata na jihar Ladi Dansure ta ce rashin kulawa da yara da wasu iyayen ke yi na daya daga cikin matsalolin dake haddasa wannan matsala.

” Da wuya mako ya wuce ba a kawoi Karan anyi wa wata fyade ba.”

Daga karshe shugaban kungiyar lauyoyi reshen jihar Jigawa Baffa Alhassan a nashi tsokacin ya yi kira ga gwamnati da su horar da ‘yan sanda kan dabarun zamani kan yadda ake hukunta wa da ceto yaran da akayi wa irin wannan mummunar aiki sannan da to wa duk wanda aka kama horo mai tsanani.

Ya kuma roki gwamnati da ta samar da asibitoci domin Kula da irin wadannan yara da suka fada irin wannan tsautsayi.

Share.

game da Author