TAMBAYA: Sunayen Annabi guda nawa ne? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Sunayen Annabi guda nawa ne?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Hakika malamai sunyi sabani akan yawan sunaye Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wa Sallam. Wannan sabanin kuma ya samo asaline daga kallon siffofin da aka siffanta shi da su, a yayin da wasu malamai ke ganin cewa siffofin annabi, sunayensa ne, wasu kuma keganin cewa ba sunayen annabi bane.

Malamai da bandaban sunyi rubuto akan sunayen Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wa Sallam, kuma sunada banbancin ra’ayi kamar haka:

1. Wasu malamai sun ce sunayen Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wa Sallam guga 99 ne.

2. Wasu malamai kuma sun kididdiga sunaye 200 a matsayin sunayen Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wa Sallam (Jazuli a cikin Dala’ilu).

3. Ibni Dahiyya kuma a cikin littafin sa Almustafa ya lissafa sunaye 300 a matsayin sunayen Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wa Sallam.

4. Wasu malaman kuwa suna ganin sunayen Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wa Sallam sunkai sunaye 1000.

Amma abinda yafi inganci da dacewa daga cikin maganganun malamai shi ne sunayen Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wa Sallam kadan ne kwarai. Kuma daga Alkur’ani da ingantatton Hadisai kadai za’a samu sunayen. Sannan kuma siffofinsa siffofi ne, ba sunaye bane.

Hadisi ya inganta acikin Bukhari, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wa Sallam ya ce: Inada sunaye Biyar: ni ne Muhammadu, da Ahmadu, ni ne Al-Mahi: wanda Allah ke share kafirci da shi, ni ne Al-Hashiru: wanda za’a tada mutane bayansa, ni ne Al-Aqibu. ( Bukhari 3532) .

Malamai suka ce dolene a nisanci kage da kirkira a cikin sunayen Annabi SAW. Dolene duk sunan da za’a jingina masa ya zamo an samo shi ne daga ingantattacen Nassin Alkur’ani da Hadisi, domin gudun fadawa cikin hadari.

GA WASU DAGA SUNAYENSA

1) Muhammadu

2) Ahmadu

3) Almahi

4) Alhashiru

5) Al-Aqibu

6) Nabiyut- Taubah

7) Nabiyur- Rahmah

8) Almuzammil

9) Almudassir

10) Albashir

11) Annadhir

12) As-sirajul Munir

13) Daha

14) Almudhakkir

15) Habibur- Rahman

16) Almusdafa

17) Almukhtar

18) Sayyidul- Mursalin

19) Sayyidu Waladi Adam

Allahumma Salli Ala Muhammad Wa Ala Ali Muhammad.

Ya Allah! Ka karamana son Annabinka, kuma ka hadamu da shi a Al-Jannarka. Amin.

Share.

game da Author