Rikicin da ya nemi tirnikewa tsakanin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Mataimakin sa, Hafiz Abubakar ya ci kujerar Shugaban Jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas.
Wani jami’an kwamishinan Yada Labaran Jihar Kano, mai suna Hafiz Alfindiki ne ya tabbatar wa PRRMIUM TIMES da saukar Abdullahi Abbas daga shugabancin jam’iyyar.
Farkon cikin makon da ya gabata ne mataimakin gwamnan ya fito ya ce ba zai tsaya takara tare da gwamna Ganduje ba a 2019, domin ba zai jure irin wulakancin da aka yi masa a mazabar sa ba.
Hafiz, wanda Farfesa ne, ya ce jam’iyyar APC ta yi sauye-sauye a cikin shugabannin mazabar unguwar sa, amma aka cire har da dan uwansa, ba tare da an sanar da shi abin da ake ciki ba.
Wannan kalami ya girgiza gwamna, inda nan take ya ce a gaggauta maida wanda aka cire, sannan kuma ya hori uwar jam’iyyar da su rika girmama mataimakin sa kamar yadda su ke girmama shi.
Ganduje ya ce ya yi mamakin abin da ya faru, domin ba shi da masaniya.
Sai dai kuma ana da tabbacin hannun shugaban jam’iyyar wanda hakan ne ya sa ya samu sabani da gwamnan, wanda ta kai shi ga sauka daga mukamin sa.
Majiya ta ce hankalin Ganduje ya tashi sosai, domin wannan sabani kan iya hana shi samun nasara a zaben 2019.
Abdullahi Abbas dai dan gaban-goshin Ganduje ne sosai. Tabbatattun hujjoji sun nuna yadda ya rika zakalkalewa wajen ganin sai an tsige Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, yayin da sabani ya shiga tsakanin sa da gwamna Ganduje.
Akwai yiwuwar Abbas zai gurfana a gaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, duk da dai babu wata bayyanannar takardar gayyatar sa zuwa majalisar.