Ku daina gyara min Turanci na – Adam Zango

0

Jarumi Adam Zango ya roki masu karatu da ke yawàn gyara masa Turanci sa Idan ya yi rubutu da suyi hakuri su dai na haka.

Adam a wata gajeruwar bidiyo da ya saka a shafin sa na Instagram ya ce ba ya kan yi rubutu don ya burge bane. Ya na haka ne domin ya isar da sakon sa ga masoyan sa da ba su Jin Hausa Kuma su basu ce ba sa ganewa ba.

Adam ya ce shi ba bature bane kuma ko Makaranta ma bai yi ba. Turancin da yake kokarin yi ma yanzu, a harkar sana’ar sa ya koyeta.

Abokan sana’ar sa da yawa sun tofa albarkacin bakin su kan haka inda suka roki Zango da ya daina amsa wa masu yi masa haka.

” Ka dai na biye musu. Amsar da kake basu ne ya sa suke ci gaba da yi maka haka.” Inji Nafeesat Abdullahi.

Share.

game da Author