Shugaban Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida, Babatunde Fowler, ya bayyana cewa hukumar sa ta kulle ofisoshi, gine-gine da gidaje 3000 a babban birnin tarayya, Abuja.
Fowler ya ce an kulle su ne saboda kasa biyan kudaden harajin 2017 da suka yi. Da ya ke magana a wani taron kwana daya kan wayar da kan mutane dangane da muhimmancin fitowa a bayyana kadarar da mutum ko kamfani ya mallaka, a yau Alhamis a Abuja, ya ce an fara kulle gidajen ne tun daga watan July na wannan shekarar.
“Mun kusan gajiya da zaman jiran da muke wa masu wadannan kadarorin fankama-fankaman gine-gine da su zo yi kawo mana bayanin kudaden shigar su tare da biyan haraji.
“Amma nan ba da dadewa ba, za mu je kotu domin kotu ta daga gine-ginen a sayar da su, mu cire kudaden harajin da ake bin mai ginin, idan sauran canji ya ragu kuma, sai a mayar masa.” Inji Fowler.
Daga nan sai ya yi karin haske da cewa, “akwai gidaje ko ofisoshi manya da aka gina da sunan mallakar kamfanoni ne, ba tare da su na biyan harajin ko sisi ba ga gwamnati. To duk wadannan manyan gidajen da duk wani fegi ko filin da masu shi su ka ki ginawa, duk za mu rika karbar harajinn gwamnati daga gare su.”
Ya ce kamar yadda tsain su ya tanadar, idan kamfani ko wani ofis ko cibiyar hada-hadar kasuwanci ta ki biyan haraji, to hukumar sa za ta cire kashi 20 bisa 100 na cinikin da ya yi a wannan shekara,ta dauka a matsayin harajin da bai biya ba.
“Idan fa ka ga kamfani ya gina rukunin gidaje, to tabbas akwai wata hanyar da kudaden suka fito. Idan mai daukar albashin naira milyan 10 a shekara ya gina gida na naira miliyan 100, to da karfin arzikin gidan sa na naira milyan dari za mu ciki haraji daga cikin sa, saboda akwai wata hanyar da kudin suka fito kenan, hanyar da ba albashin sa ba.
Idan ba a manta ba, gwamnatin Najeriya ta umarci Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Kasa, FIRS da ta tara kudaden haraji na akalla naira tiriliyan 4.93 a cikin wannan shekara mai kamawa.
Discussion about this post