MATSALAR LIBYA: Alhakin kisan-walakancin da aka yi wa Ghaddafi ne -Femi Falana

0

Lauya mai rajin kare hakkin bil’adama, Femi Falana, ya bayyana cewa abin da ke faruwa yau a Libya inda ake bautar da daruruwan ‘yan Nijeriya da sauran ‘yan kasashen Afrika a Libya, ya ce Nijeriya ce ta janyo musu wannan bala’i.

A cikin wata doguwar takarda da lauyan ya rubuta kuma aka buga ta yau Alhamis a PREMIUM TIMES, ya bayyana cewa Nijeriya ta ki sauraren su, ta biye wa Amurka da wasu dibgaggun manyan kasashen Turai ido-rufe, aka goya wa ‘yan tawayen Libya baya aka kifar da gwamnatin Ghaddafi.

Ya ce kowa ya san Amurka da kasashen Turai sun yi haka ne domin su rika samun man kasar Libya a saukake. Ya ce a yau ana yawan jigilar man Libya zuwa Turai da Amurka, amma Najeriya ba ta amfana da komai ba, sai muggan makaman da ‘yan tawayen suka yaki gwamnatin Ghaddafi wadanda kowa ya tabbatar da cewa su ne aka rika saida wa Boko Haram, shi ya sa har yanzu kungiyar ta gagara a kasar nan.

Falana ya ce Ghaddafi ya kasance bangon jinginar kasashen Afrika. Amma wadanda ba su yarda da wannan ba a da can, yanzu tilas idan an fada su yarda, domin an rigaya an kashe shi, kuma an kashe kasar Libya.

Ya kara da cewa a yanzu Libya babu takamaiman gwamnati, ‘yan tawaye sun kasu gida biyar, kowane bangare na ikirarin shi ke da Libya.

Lauyan ya ce ba zai taba mantawa ba cikin 2009, lokacin Ghaddafi shi ne shugaban kungiyar kasashen Afrika. An yanke wa wasu ‘yan Najeriya su 200 hukuncin kisa a kasar. Falana ya ce a matsayin su na kungiyar masu kare hakkin bil’adama a Afrika, sun yi roko ga Ghaddafi da ya dubi Allah, kuma ya nuna tausayi, kada a kashe su.

“Ni ne da kai nan a yi wannan roko ga Ghaddafi. Abin mamaki, duk da zafin sa, sai ga shi ya saurari kukan mu, ya janye hukuncin kisan, sannan kuma ya yi musu afuwa, aka sake su.” Inji lauya Falana.

Ya kara da cewa to da Najeriya ta daure gindi aka kashe Ghaddafi da Libya, wace riba ta samu a yau, in ba Boko Haram ba?

Share.

game da Author