Najeriya ta bukaci a sauya fasalin Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya

0

Najeriya ta bukaci a gaggauta sauya fasali tare da kara yawan mambobin Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya, domin a kawar da rashin adalcin da ake nuna wa Afrika a cikin wannan majalisa mai mambobi 15 kacal.

Babatunde Nurudeen ne ya gabatar da wannan matsaya ta Najeriya. Nurudeen shi ne wakilin Najeriya na dindindin a Kungiyar Kasashe Afrika ta Yamma, a Majalisar Dinkin Duniya. Ya yi jawabi ne a batun Yiwuwar Samun Wakilcin da ya Dace da Yiwuwar Kara Yawan Mambobin Majalisar.

Majalisar Tsaron it ace majalisa mafi karfi a Majalisar Dinkin Duniya, kuma it ace kula da rikice-rikice da sauran su. Ita ce kuma ke kafa rundutsar tabbatar da tsaro ta majalisar dinkin duniya. Sannan kuma ita ce ke rattaba hannun amincewa da duk wata doka kon yarjejeniya ko sharudda.

Majalisar ce kuma ke da ikon sanya takunkumi, cin tarar wata kasa ko tura mata dakaru idan hakan ta kama.

Nurudeen ya ce abin takaici ne tun shekaru 72 da suka gabata, an maida Afrika saniyar-ware ba ta da wakilci a majalisar, duk kuwa da karfin iyawa da cancantar da ta yi.

Share.

game da Author