Malamin koyar da tukin mota ya kashe wata ‘yar bautar kasa bayan yayi lalata da ita

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani malamin koyar da tukin mota mai suna Festus Udo da laifin aikata fyade da kisan wata dalibar sa dake bautan kasa a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmed Ilyasu wanda ya sanar da haka wa manema labarai ya ce tun bayan ofishin su ta sami labarin bacewar yarinyar mai suna Modupe Taiyese ‘yar shekara 23 daga ofishin hukumar NYSC na jihar suka fantsama neman ta babu kakkautawa.

Ya ce sun kama Festus ne da aikata wannan laifi bayan gano lambar wayar sa da su yi daga wayar mamaciyar a matsayin wanda ta kira na karshe kafin ta bace.

” Nan da nan muka fara tambayar sa kan wannan mamaciyar inda ya furta da bakin sa cewa shine ya yi sanadiyyar ajalin ta.”

Iliyasu ya bayyana cewa Festus malamin koyar da tukin mota ne a makarantar koyan tukin mota na ‘Lizzy Driving School’ dake Abeokuta kuma shine malamin dake koyar da mamaciyyar Madupe tukin mota.

Ya ce Festus ya kashe mamaciyar ne bayan ya kira ta waya ranar Asabar ta zo ta karbi lasisin tukin ta daga wajen sa.

” Ko da Marigayiya Madupe ta zo sai Festus ya lallabe ta ya kai ta dajin Abule dake kauyen Mawuko a karamar hukumar Odeda na jihar inda ya sami nasaran danneta da karfin tsiya sannan ya kashe ta bayan haka.”

“Festus ya shake mamaciyar ne bayan ta yi barazanar kai karan sa wajen iyayen ta.”

Share.

game da Author