Kotu ta hana belin Maryam da ake tuhuma da kashe mijin ta

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta hana belin Maryam Sanda, surukar tsohon shugaban jam’iyyar PDP.
Maryam na fuskantar tuhuma da kashe mijin ta Bilyaminu Bello a cikin watan Nuwamba.

Ana tuhumar ta tare da mahaifiyar ta, Maimuna Aliyu, sai dan uwanta Aliyu Sanda, da kuma ma’aikaciyar gidan mai suna Sadiya Aminu. Ana tuhumar sauran ukun da laifin hada baki da Maryam domin su rufa aika-aikar da ta tafka.

Lauyan wadda ake tuhuma, Joseph Daudu, ya nemi kotu ta ba shi belin ta, a kan dalilin cewa Maryam ta kawo takardar binciken likita mai nuna cewa ta na bukatar kulawa da lafiyar ta, wanda ba za ta iya samun haka ba a inda ta ke a tsare.

Daudu ya buga misalai da hujjoji daga cikin dokokin kasar nan masu nuni da cewa mai matsalar rashin lafiya kamar ta Maryam, gami da yadda ta ke jegon yarinya ’yar wata takwas, ita kan ta yarinya na bukatar kulawar mahaifiyar ta sosai.

Sai dai shi kuma Babban Mai Shari’a Yusuf Halilu, ya bayyana cewa sashen dokar da Daudu ya kawo a matsayin hujja, ta na nuni ne da cewa sai idan tabbas yin hakan ne kadai mafita. To amma hujjar da lauya Daudu ya gabatar, Yusuf ya ce ba su tabbatar da cewa bayar da belin Maryam shi ne kadai mafita ba.

Alkalin ya kara da cewa, duk da dai batun bayar da beli ya na hannun kotu ba wani ba, akwai wasu sabubba uku da kotu ke dubawa kafin ta bayar da beli.

“Duk da cewa sahe na 36 (5) na dokar Nijeriya ya ce wanda ake zargi ba shi da laifi, har sai kotu ta tabbatar a aikata laifin a kansa, to ita kotun za ta kalli batun bayar da belin ne a shar’ance kuma a cikin adalci ga kowane bangare.

“Irin laifin da ake tuhumar ta da shi, da kuma hujjojin da ke a gaban kotu da kuma hukuncin da ka iya biyo baya idan har an kama ta da laifi, to abin dubawa ne matuka a daya bangaren.

“Sannan kuma tilas sai idan akwai cikakkar hujja mai kwarin gaske da ke nuni da cewa wadda ake tuhumar na fama da ciwon da ba a iya kulawa da ita idan ta na tsare, ko kuma ba za a iya samar mata magani idan ta na tsare ba.

“Daga nan inda na ke ina kallon wacce ake tuhumar da ke can a tsaye, da ganin ta kai ka san akwai alamun karfi a jikin ta. Ga ta nan fa a tsaye gaban kotu sama da awa daya ta na tsaye, ba ta nuna gajiyawa ba.

A karshe ya hana belin Maryam amma ya bayar da belin sauran ukun da ake tuhuma, ganin cewa su ne su ka kai kan su kotun, ba kamo su aka yi ba.

Sai dai belin na tare da sharadin cewa wadanda za su yi belin na su ya kasance mazauna Abuja ne, kuma kowanen su na da gida a Abuja.

Alkalin ya kuma umarci su kawo fasfo din su na iznin fita kasar nan kafin a bayar da belin na su.

An daga karar zuwa ranakun 5, 6 da 7 Ga Fabrairu.

Share.

game da Author