Shugaban EFCC, Ibrahmim Magu, ya bayyana cewa babu wata rashin jituwa tsakanin hukumar sa da SSS da kuma NIA.
Magu ya tsaya a kan wannan matsaya ne, dangane da wani bayani da shugaban kwamitin majalisar dattawa da zai binciki sabanin da ke tsakanin hukumomin tsaron uku, Sanata Francis Alimikhena ya furta.
Alimikhena ya jajirce cewa ya na so a saurari zaman binciken a gaban ’yan jarida domin kowa ya ga abin da za a tattauna a kai.
“Ni ban ga wani abin biyewa game da zaman kwamitin ba, domin hukumomin sun keta wa juna sutura a bainar jama’a. Me ya rage da za mu boye kuma? Ai tunda sun yi fada a bainar jama’a, gara su fito su fada mana dalilin fadan na su.
Sai dai kuma Sanatan shi kadai ne daga cikin mambobin kwamitin sa biyar mai son a yi zaman a bainar jama’a.
Amma kuma shuagabn EFCC, Magu ya ce masa ai babu wani batun yaga wa juna sutura da suka yi a tsakanin hukumomin tsaron biyu.
“Mai Girma Shugaban Kwamiti, ni dai ban san da wani fada a bainar jama’a da mu ka yi a tsakanin mu ba. Kuma hukuma ta ba mu yi fada da wata hukuma ba.
“Abin da na sani kawai shi ne, yara na sun je domin su yi kame, kuma sun je ne tare da takardar iznin su yi kamen, amma aka hana su kama wadanda su ka je kamawa.”
A karshe dai an amince za a yi zaman a asirce. Amma kuma za a kira kowace hukumar tsaro daban ita kadai, daya bayan daya. A bisa sharadin cewa da EFCC za a fara gayyata.
Idan za a iya tunawa, PREMIUM TIMES ta kawo rahoton yadda EFCC ta je kama tsoffin daraktocin hukumar NIA da DSS, amma aka ta kama su.