Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rawaito cewa cikin mutane 43,806 da suka mika takardun su don neman aikin malunta a Kaduna har da masu takardun shaidar kammala karatu na digir-gir wato Masters Degree.
Jami’a a hukumar kula da ilimi na jihar Kaduna Mary Ambi ta ce wadanda suka sami nasarar cin makin da aka kayyade ne za a tuntuba domin yi musu gwaji na gaba da gaba.
Idan ba a manta ba a watan Yuni gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta sallami dakikan malamai da basu ci jarabawar gwaji ba da gwamnati ta yi wa malaman.
Sama da malamai 21,000 ne suka fadi jarabawar gwajin.
Sai dai kuma wata hanzarin ba gudu ba, kotu a jihar ta dakatar da wannan sallama da gwamnatin ke shirin yi wa malaman jihar, bayan karar da wani lauya ya shigar gaban ta cewa ba a bi yadda doka ta gindaya ba wajen shirya jarabawar gwajin.
Za a ci gaba da shari’ar a watan Fabrairun 2018.
Discussion about this post