BAKON DAURO: An yi wa yara miliyan 1.6 allurar rigakafi a Barno

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Borno Haruna Mshelia ya ce gwamnatin jihar ta yi wa yara miliyan 1.6 allurar rigakafin cutar bakon dauro a jihar.

Ya fadi haka ne a lokacin da yake ganawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN inda ya kara da cewa sun yi wa yaran alluran ne a karo na faro da na biyu.

Ya ce a karo na farko sun sami nasarar yi wa kashi 92 bisa 100 na yaran kudanci jihar sannan a karo na biyu kuma sun yi allurar ne a arewacin yankin jihar da kananan hukumomi 4 da ke tsakiyar jihar.

Bayan haka Mshelia ya sanar da cewa sun yi wa mutane miliyan daya alluran rigakafin cutar kwalara a watanni uku da suka gabata.

Daga karshe Mshelia ya ce tare da hadin guiwar WHO da sauran kungiyoyin bada tallafi sun sami nasaran dakile sake bullowar cutar a jihar.

Share.

game da Author