Jami’an tsaro a Kano sun ceto wani yaro dan shekara uku da kayi garkuwa da shi bayan wani samame da suka kai maboyar barayin yaran.
Mahaifin yaron ne ya sanar wa ‘yan sanda bacewar dan sa sa, da yayi kwanaki 11 a wajen barayin.
Suko jami’an tsaro suka fantsama neman sa, cikin ikon Allah kuwa sai suka gano cewa yaran na kusa da gida domin barayin ma makwabtan yaron ne.
Mahaifin yaron ya sanar wa jami’an tsaro cewa barayin sun nemi ya biya naira miliyan 20 ne da farko. Da ya nemi sassauci sai suka rage zuwa naira N200,000.
Barayin da aka kama sun hada da wani dan shekara 17 mai suna Abba Tijjani, da wani Jamilu Alhassan da Umaru Salisu mai shekaru 27.
An sami sauran kudin da aka biya na fansar yaron da bindigar roba, wuka da abin badda kama.
Daya daga cikin barayin Salisu Umaru ya ce sun fada wannan mummunar sana’a ne bayan yawan kallon fina-finan kasashen waje.