Majalisar Kaduna ta dakatar da wasu mambobi biyu haka kawai

0

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta dakatar da wasu ‘yan majalisa biyu, Bityong Nkom (PDP-Kaura) da Danladi Kwasu (PDP- Zangon Kataf) haka kawai.

Majalisar ta yanke wannan shawara ne bayan gabartar da hakan da dan majalisa mai wakiltan Doka Gabasawa, Mukhtar Hazo yayi a zauren majalisar.

Hazo ya sanar wa majalisar cewa yan majalisar biyu na yin wani abu da bai fadi ko menene ba da zai iya yada darajar majalisar a idanun mutane.

“ Saboda haka ne na ke kira ga majalisa da ta dakatar da wadannan ‘yan majalisa biyu. Abdulrahman Haruna ya amince da wannan kira daga nan kuwa sai shugaban majalisar Aminu Shagali ya sanar da dakatar da mambobin biyu.

Dukkan su biyu sun nemi a fadi wa duniya abin da suka yi amma shugaban majalisar Shagali ya umurci masu kula da majalisar su fita da su daga zauren majalisar sannan ya daga zaman majalisar zuwa Talata mai zuwa.

Share.

game da Author