Sanata Ben Murray-Bruce, mai wakiltar Bayelsa ta Gabas, ya yi kakkausar suka ga Gidan Talbijin, Gidan Radiyon Najeriya da kuma Muryar Najeriya cewa duk ba su da amfani, kamata ya yi kawai a sayar da su.
Bruce ya ce wadannan kafafen yada labarai na gwamnatin tarayya ba su da wani tasiri a zukatan ‘yan Nijeriya, idan aka sayar da su, za a rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa a cikin kasafin kudin shekara-shakara wajen tafiyara da su.
Sanatan ya bayyyana wannan shawara ce tasa yayin da Majalisar Dattawa ke zaman muhawara a kan kasafin 2018.
Ya ci gaba da cewa hanyoyin da gwamnati ke kashe kudade sun yi matukar yawa, don haka akwai bukatar a gaggauta rage hukumomin da ba su da wani amfani ga ci gaban kasa.
“ “A ko da yaushe mu na kasa cim ma yawan kudaden shigar da mu ke so mu samu a shekarar kowane kasafin kudi.
“Idan ka kalli kasafin kudi tun daga 1960 zuwa na bana, akwai wasu hukumomin da aka kafa saboda farfagandr Yakin Basasa. Amma ga shi shekaru sittin kenan har yau ana amfani da wasu da aka kirkiro tun wancan lokacin. Sun zame wa kasafin kudi karfen-kafa kawai.
“Na yi waya da Obasanjo a kwana biyu da suka gabata cewa Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta na da amfani, amma a lokacin da ba mu da jam’iyyun siyasa. Na ce masa a wannan zamanin na yau, mene ne amfanin Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa? Amma kuma ana kashe wa hukumar nan bilyoyin kudade a kowace shekara.
“Dubi hukumomi irin su Gidan Radiyon Najeriya, ta na da ma’aikata 8,000. To a saida wa Ma’aikatan hukumar a huta kawai mana. Ita ma NTA a saida ta ga ma’aikatan ta, haka Muryar Najeriya. A yi kamar yadda Awolowo ya taba yi. Amma idan har za mu ci gaba da kashe kashi 71 cikin 100 na kasafin kudi kan ayyukan yau da kullum, to ba za mu taba fita daga halin-kaka-ni-ka-yi ba,
Discussion about this post