Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya ce yawan tattauna batun zaben 2019 da ake ta yi a yanzu bai dace ba, domin ya na dauke hankunan masu rike da mukamai a yanzu.
Da ya ke magana da ‘yan jarida a Sokoto, Tambuwal ya ce abin da ya dace a rika magana a yanzu shi ne yadda shugabanni ke gudanar da abin da aka zabe su a 2015 su yi.
“Ban san dalilin da ya sa ku ke tambaya a kan zaben 2019 ba, a lokacin da ba mu dade da wuce rabin zangon shekarun hudu ban a wa’adin zaben 2015.
“Masu rike da mukaman siyasa na bukatar a rika tattauna abin da shugabancin da suke yi ya sa a gaba. Amma yayin da ka ke maganar zaben 2019 a cikin 2017, to fa ka na dauke masa hankali ne kuma ka na rudar da tafiyar siyasa a tsarin shugabancin da aka damka wa wadanda aka zaba a matsayin amana.
Tambuwal ya ce gwamnatin sa za ta kara bada himma wajen inganta harkokin noma da sauran hanyoyin inganta kasuwanci da tattalin arziki.
Discussion about this post