Majalisa ta hana a koya wa sojoji Hausa, Yarbanci da Igbo

0

Majalisar Tarayya ta yi watsi da wani shiri da hukumar tsaro ta sojoji ke yi domin koya wa sojoji yaren Hausa, Yarbanci da Igbo.

An yi watsi da wannan tsari ne a yau Laraba a zaman da majalisar ta yi.

Daga nan sai ‘yan majalisar suka nemi da Hafsan Askarawan Najeriya, Tukur Buratai da ya dakatar da shirin da zai fara na tilasta wa sojoji koyon manyan yarukan na kasar nan uku.

Wani dan majalisar tarayya ne mai suna Abiante Dagomie da kuma Diri Douye suka gabatar da kudirin bukatar a dakatar da shirin, kuma a nan take wadanda ba su goyi bayan shirin ba suka yi rinjaye a majalisar.

Hon. Dagomie ya ce tilasta wa sojoji koyon yarukan guda biyu, tauye musu hakki ne, domin kasar nan na da yaruka da yawan gaske, su ma an tauye su kenan.

“Don me za a fifita yare uku kacal a cikin yarukan kasar nan sama da 400?”

Share.

game da Author