Hukumar Kwastam ta kama mota make da Shinkafa a iyakar Sokoto

0

Hukumar kwastam da ke kula da shiyar Sokoto, Kebbi da Zamfara ta kama wata mota dankare da buhunan shinkafa 506 da aka hana shigowa da su kasar nan a iyakar Sokoto- Illela ranar Juma’a.

Shugaban hukumar dake kula da wannan shiya Nasir Ahmed ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a Sokoto.

Ya ce buhunan shinkafar za su kai Naira miliyan 12.5. Sannan ya ce hukumar sa ba za tayi kasa-kasa ba wajen ci gaba da farautar irin wadannan masu yin fasakwaurin a iyakokin jihohin nan.

Daga karshe Ahmed ya yi kira ga mazaunan kusa da iyakokin da su hada hannu da hukumar wajen hana shigowa da kayakin da gwamnati ta hana shigowa da su musamman ganin cewa ya na daga cikin ababen da ke karya tattalin arzikin kasa.

Share.

game da Author