Hukumar Alhazai na jihar Katsina ta sanar da naira 300,000 kudin fara tari

0

Gwamnatin jihar Katsina ta ce maniyatan aikin hajji badi daga jihar za su iya fara tara kudin aikin hajjin yanzu.

Duk wani maniyyaci ko Maniyyaciya zai ko za ta iya fara ajiya daga Naira 300,000.

Shugaban hukumar kula da jin dadin mahajjata na jihar KSPWB Muhammad Abu-Rimi ya sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba a Katsina.

Ya ce sun yi haka ne domin yin biyayya ga umurnin da hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta bada game da haka.

Abu-Rimi yace maniyatan za su fara tara wannan kudi a banki daga watan Nuwamban wannan shekaran zuwa watan Maris 2018.

Ya ce yayin da maniyatan za su ziyarci ofisoshin su domin yin rajista ba za su karbi tsabar kudi ba sai dai takardan nuna shaidan biyan kudi a banki wato ‘Bank Draft’.

” Sauran abubuwan da za mu bukata sun hada da hoto fasfo, takardar shaidar karamar hukumar ka na asali sannan mace ta zo da muharramin ta.”

Daga karshe Rimi ya ce wandanda suka yi aikin Hajji sau biyar ko kuma kasa da haka za su biya karin Naira 163,000 kan kudin tafiya hajin da hukumar NAHCON za ta sanar nan gaba.

Share.

game da Author