KISAN FULANI A NUMAN: Dole a sake lale – Sarkin Musulmi

0

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi Allah-wadai da kisan da ka yi wa Fulani a yankunan Numan cikin Jihar Adamawa.

Sarkin Musulmin ya yi gargadin cewa shiru-shirun da Fulani ke yi fa ana ta kisan ’yan uwan su a Adamawa, ba fa tsoro ba ne ko ragwanci.

Daga nan sai ya yi kira da a yi kwakkwaran binciken kashe-kashen Fulani a kauyuka hudu na Numan a jihar Adamawa, inda aka yi zargin cewa kabilar Bachama ne suka yi kisan.

Har yanzu dai babu wata kabila da ta fito ta ce ita ce ta yi kashe-kashen.

Sarkin Musulmi ya yi wannan gargadi ne a Yola, jiya Lahadi, a lokacin da ake kaddamar da gidan radiyon Pulaaku FM wanda mallakin Lamidon Adamawa, Barkindo Mustapha ne.

Sultan ya yi tir da kisan da aka yi wa har da mata da kananan yara a garuruwan Shaforon, Kikem da Kodemti a Numan.

Share.

game da Author