2019: Kada Buhari sai an yi taron-dangi – Doyin Okupe

1

Tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan kan harkar hulda da jama’a, Doyin Okuope, ya bayyana cewa kamata ya yi jam’iyyun adawa su hadu tare da hada karfi wuri daya domin a kayar da jam’iyyar APC a zaben 2019.

Okupe ya yi gargadin cewa jam’iyyar PDP ita kadai ba za ta iya kayar a Shugaba Muhammadu Buhari ba idan ta ce ba za ta nemi hadin kai da wasu jam’iyyu ba.

Okupe dai a yanzu shi ne shugaban jam’iyyar AP, wato Accord Party, bayan ya fice daga PDP cikin shekarar da ta gabata.

Ya yi wannan jawabi ne a Ado-Ekiti, jihar Ekiti ranar Asabar da ta gabata.

“Sai da aka yi taron-dangi kafin a kori sojoji daga mulki aka dawo da dimokradiyya cikin 1999. Wannan taron-dangin ne ya rikide ya zama PDP inda ta ci zabe ta yi mulki har tsawon shekaru 16.” Inji Okupe.

“Haka ma sai da aka yi taron-dangin jam’iyyu a 2015, sannan aka kwace mulki daga PDP.”

Okupe ya ce ficewar Atiku daga APC, ya tabbatar da cewa jam’iyyar na cikin matsala sosai, kuma da wuya ta sake cin zabe a 2019, musamman idan jam’iyyu suka hadu aka yi mata taron-dangi.

Share.

game da Author