Gobara ta lashe dakunan mata a Kwalejin Gwamnati ta Keffi

0

Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya ruwaito cewa wata gobara da ta tashi da misalin 7:45 na daren jiya Lahadi, ta lashe dakuna biyu na dalibai mata a makarantar sakandare ta Keffi, jihar Nassarawa.

Rahoton ya ce wutar sai da ta kai wayewar garin yau Litinin ta na ci ba a samu kashe ta ba, kuma ta yi wa dakunan kurmus.

“ Wasu dalibai na can dakin cin abincin dare a lokacin da gobarar ta tashi. Wani babban malamin kwalejin ya ce littattafai da sauran kayan da daliban suka mallaka duk sun kone, ba a cire ko tsinke ba. Sai dai kuma ba a samu rahoton salwantar rai ko da yaba.

“Akwai dai wata daliba da ke kwance ta na barci, a lokacin da gobarar ta tashi, amma ta ji raunuka a lokacin da ta tsallaka ta taga ta dira waje.”

Mataimakin Shugaban Kwalejin, Gideon Gutap, ya shaida wa NAN cewa har yanzu dai ba su yanke shawarar matakin da za a dauka ba tukuna.

Gobarar dai ta tashi ne kwana daya kacal kafin a fara jarabawa.

Share.

game da Author