Dalilin da na ki sa hannun kafa Jami’ar Wukari – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana wa Majalisar Tarayya dalilin sa na kin sa wa dokar kafa Jami’ar Wukari hannu.

A cikin wasu wasiku mabambanta da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, da Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, Buhari ya ce ya yi haka ne saboda an bayyana wasu bayanai ba daidai ba a cikin kudirin da ya maida kafa jami’ar zuwa doka.

“Misali, wadansu wuraren da aka baddala bayanai sun hada sakin layi na 9, inda aka rubuta “maziyarci, maimakon shugaban kasa.”

“An kira karamin sakin layi na 2, a matsayin na 3.” Kenan na 3 aka rubuta, maimakon na 2.

Share.

game da Author