An yi muhawara don samar wa fannin kiwon lafiyar karin kudade a kasafin 2018

0

Kungiyar hadin guiwa da ke Kula da lafiyar Yara da iyali ‘Partnership for Advocacy in Child and Family Health at Scale, PACFaH’ ta gudanar da wani taron sanin madafar aiki da ganawa da wasu Kungiyoyin kiwon lafiya don ganin yadda za a Samar wa fannin Karin kudade a kasafin kudin Kasar nan.

Kungiyar PACFaH ta ce a kasafin kudin shekarar badi gwamnatin tarayya ta Samar da kashi 3.9 bisa 100 cikin kasafin kudin. Hakan zai sa fannin ta yi fama da karancin kudade da za ta gudanar da ayyukan ta a shekarar.

Da yake tofa albarkacin bakin sa a taron shugaban Kungiyar’NACHPN Ibama Asiton ya koka kan yadda kudaden da ake samun raguwa kan kudaden da ake ware wa fannin kiwon duk shekara a kasar nan.

Ya ce hakan ne ya sa suke jawo hankalin gwamnati don kara yawan kudade da take ware wa fannin kiwon lafiya a kasafin Kasa.

” Kamar yadda bukatun kasa yasa aka samu kari a kasafin kudi daga Naira Tiriliyan 4.49 a shekaran 2015 zuwa naira 8.16 a shekaran 2018 haka ya kamata na fannin kiwon lafiya ya karu.”

” Ya kamata mu tambayi kan mu game da yawan kudin da gwamnati ta ware wa fannin kiwon lafiya, shin zai isa a iya amfani da shi wajen aiwatar da aiyukkan da ya kamata sannan gwamnatin za ta iya farfado da cibiyoyin kiwon lafiya 10,000 da take burin yi, ko a’a?”

Wani da ya halarci taron yayi tambaya cewa wani kokari akeyi wajen ganin gwamnati ta cika alkawuran ta wajen ware isassun kudade wa fannin kiwon lafiya.

Shugaban kungiyar NACHPN reshen yankin arewa maso gabacin kasan Yakubu Zaakshi y ace suna iya kokarin su wajen ganin hakan ya yiwu amma ya ce har yanzu akwai sauran aiki a gaban su game da hakan.

” Za mu yi kokarin ganin mun wayar wa gwamnati kai don ganin ta kara yawan kudaden wa fannin kiwon lafiya a kasafin kudin ganin cewa har yanzu ma ba a fara zama akan kasafin kudin ba.”

Share.

game da Author