Yadda Malami da Dambazau suka maida Maina aiki bayan kasurgumin mai laifi ne

0

Abu dai kamar almara, sai gashi bayanai suna ta fitowa game da yadda tsohon shugaban kwamitin shugaban kasa na gyaran fansho Abdulrasheed Maina ya koma aikin gwamnati bayan hukumar EFCC na neman sa ruwa a jallo.

Ana farautar Maina ne bayan gano cewa da hannun sa dumu-dumu a harkallar wasu kudade da ya kai Naira biliyan 2 a lokacin yana shugabantar wannan kwamiti.

Tona asirin sake dawowa da Maina aiki ke da wuya Ministocin da ake ganin sune ke da hannu wajen yin hakan suka fara wanke kan su.

Shi dai Maina an nada shi ne mataimakin babban darekta a ma’aikatan harkokin cikin gida.

Bisa ga sahihan bayanan da gidan jaridar PREMIUM TIMES ta bankado ya nuna cewa ministan Shari’a Abubakar Malami ne silar dawowa da Maina aikin gwamnati.

Bayanan sun nuna sannan sun tabbatar da duk kokarin da yayi domin ganin Maina ya koma aiki.

Takardun bayanan da muka samu ya nuna yadda Malami a matsayin sa na ministan Shari’a ya yi ta amfani da kujerar sa domin ganin hakan ya tabbata.

Tun 27 ga watan Afirilu ne shirin haka ya dauko asali inda Malami ya rubuta wa hukumar daukar ma’aikata na gwamnatin tarayya da kada su ci gaba da dogara da hukuncin wata kotu da ta yanke kan shi Maina wanda ya yi sanadiyyar korar sa da akayi. Shugaban ma’aikatan, FCSC Suleiman Mustapha ne ya fadi haka.

Dalilin haka ne fa ita Ma’aikata Harkokin Cikin Gida a wani zaman ta musamman domin tattaunawa kan bukatar ministan Shari’a game da wanda shi kansa ministan Harkokin Cikin Gida Abdulrahman Dambazau ya jagotanta suka amince da dawo da Abdulrasheed Maina.

Duk da cewa ita ma shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya Oyo ta ce ba ruwan ta a wannan badakala, duk da haka bayanai sun nuna cewa maganar ya biyo ta ofishin ta sai dai bata ce ko mai ba wanda shine yasa babu koda fallen takarda daya ne da za ace an samu ta sa hannu ko ta yi magana a kai.

An riga an kwace wani katafaren gida nasa da akayi mata kudi ta Dala miliyan biyu, sannan bayan umarnin da Buhari ya bada a sallami Maina da ga aiki an mika masa bayanai akan yadda akayi aka maida shi aikin gwamnati.

Wani babban Lauyan gidan jaridar PREMIUM TIMES shima mai suna Jiti ya ce doka bata halasta wa shugaban kasa ikon koran ma’aikaci kamar haka ba, sai da zai iya koran Ministocin sa.

Share.

game da Author