2019: Sule Lamido ya sanar wa PDP bukatar tsayawar sa takarar shugaban kasa

0

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido ya shaida wa ilahirin mambobin jam’iyyar PDP, kyakkyawar aniyar sa ta neman fitowa takarar shugaban kasa a karkashin PDP.

Vanguard ta ruwaito daga wasikar Lamido ya shaida wa PDP cewa, abin da kawai kasar nan ke bukata shi ne a kwace mulki a hannun APC, domin a saisaita komai a kan turbar da ta dace a 2019.

Da ya ke nuna takaicin yadda kasar nan ta baude daga kyakkyawan bigire da turbar da magabatan PDP na farko su ka dora ta, sai ya ce PDP na da bukatar ganin lallai ta maida kasar nan a kan hanya mai bullewa.

“Yau shekara 57 kenan da samun ‘yanci, yanzu saboda Allah za mu iya cewa mun kai gacin da magabatan mu su ka yi kudirin mu kai ya zuwa yanzu?

To a ina da ina ne mu ka gaza cimma kudirorin mu? Kuma daga ina ne mu ka fara sakin layi? Babu wani dalili ko uzirin da Nijeriya za ta iya dogaro da shi ta ce shi ne ya hana mu ci gaba. Domin idan aka yi la’akari da albarkatun da kasar nan ke da shi, babu dalilin da zai sa mu gaza kaiwa gaci.”

“Mun kasa magance kalubalen cikin gida, na nan Afrika ta Yamma da kuma na bai daya. Babban abin takaici ma shi ne yadda kalubayen ke neman zame mana karfen-kafa.”

Don haka tilas PDP ta tashi zaye domin ta ceto kasar nan, ta maida ta kan kyakkyawa, ingattacciya kuma madaidaiciyar hanyar tsallawa tudun-mun-tsira.”

Lamido ya ci gaba da rubuta wa jam’iyyar cewa: “To dalilin wadannan kalubalen da na san zan iya bugun gaba na fuskanta ne ya sa na ke gabatar muku da kaina, domin ku amince min na fito takarar shugaban kadar Nijeriya a zaben 2019 a jam’iyya ta mai albarka.

Ban ce ni kadai ne mutumin da ya fi cancanta ba, duk wani dan PDP da za a ba wannan nauyin, zai iya tsaya mana takara. Kuma ina sa ran wasu ‘yan takarar za su nuna sha’awar su ta neman tsayawa.”

Sule Lamido na daya daga cikin wadanda su ka kafa jam’iyyar PDP a kasar nan.

Lokacin da ya ke gwamnan jihar Jigawa, ya gina gidajen saukar manyan baki har guda 17, wadanda ya sa wa su sunayen mutane 17 da su ka fara taron kafa PDP.

Ana yi wa Lamido kallon gwamnan da ya fi kowane gwamna gudanar da ayyukan ci gaba da kuma raya birane da karkara a tsakanin 2007-2015.

PDP dai ta ce takarar 2019 ta dan Arewa ce. Fitowar da Gwamna Fayose na Ekiti ya yi, bai samu kyakkyawar tariya daga jam’iyyar ba.

Share.

game da Author