Sanata mai wakitan Kogi ta Yamma, Dino Melaye ya ce sanatoci 40 sun tallafa wa ma’aikatan jihar Kogi da buhunan shinkafa 1,260 da wasu kayan abinci bayan labarin kashe kai sa da wani ma’aikacin jihar yayi sanadiyyar rashin biyan sa albashi.
Melaye ya ce sanatocin sun yi hakan ne don sauwake wa ma’aikatan jihar wahalhalun da suke ciki.
” Bayan mutumin da ya kashe kansa wani ya rasa dansa saboda ba shi da Naira 3000 kudin asibitin.”
Yayi kira ga gwamnatin jihar da su mai biya ma’aikatan jihar da ‘yan fansho kudaden su da yake wata na 11 kenan.
Discussion about this post