Allah ya yi wa matar tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata da ke wakiltan Gombe ta tsakiya sanata Danjuma Goje, Yelwa Goje rasuwa.
Daya daga cikin ‘ya’yan sanata Goje, Ahmed Mohammed ne ya sanar wa manema labarai.
Ahmed yace mahaifiyar su Hajiya Yelwa ta rasu ne a asibiti a Kasar Amurka.
Hajiya Yelwa ta rasu ta bar mijinta Danjuma Goje, ‘ya’ya 6, jikoki 10 da ‘yan uwa da dama.