Jakadan kasar Canada a Najeriya Christopher Thorney ya ce gwamantin Kasar ta bada dala biliyan 3.5 domin inganta kiwon lafiyar yara da mata a Najeriya.
Jakadan ya sanar da haka a taron samun madafa da wayar da kan mutane kan ilolin cututtukan dake kama yara kanana.
Ya ce wannan karon shirin agajin ya shafi shirin inganta kiwon lafiyar mata da yara har na tsawon shekaru 5.
Daga karshe Thorney ya jinjina wa Najeriya kan matakan da ta ke dauka don ganin an samu raguwar mutuwa da ake samu musamman ga yara kanana da mata.
Ya Kara da cewa bar yanzu akwai sauran aiki.