Najeriya ta yi asarar Dala Biliyan 13.7 sakamakon fadan Fulani da makiyaya – Abdulsalami

0

Tsohon Shugaban Kasa Abdulsalami Abubakar, ya bayyana cewa Najeriya ta yi asarar Dala bilyan 13.7 sanadiyyar fadace-fadace tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma a jihohin Kaduna, Benue, Nasarawa da Filato.

Ya yi wannan bayani ne yayin da ya ke jawabi a wurin taron hadin gwuiwa tsakanin Kungiyar Cimma Daidaiton Ra’ayi ta Najeriya da kuma Cibiyar Inganta Zaman Lafiya ta shi Abdulsami Abubakar din.

Taron dai an shirya shi ne musamman saboda makiyaya da manoma a katafariyar gonar nan mai suna Maizube Farm da ke Karamar Hukumar Bosso ta jihar Neja.

Taron na kokarin kamo bakin zaren rashin jituwa domin kawo karshen tashe -tashen hankula tsakanin makiyaya da kuma manoman kasar nan da ma sauran kasashe baki daya.

Abubakar ya kara da cewa sama da mutane 62,000 su ka rasa muhallan su a jihohin Benue, Kaduna, Filato da Nassarawa a tsakanin 2015 zuwa 2017. Yayin da akalla a cikin wannan lokacin an kashe mutane 2500 a fadin kasar nan sanadiyyar wannan rikici.

Rikicin Fulani makiyaya da manoma a kasar nan ya zama karfen-kafa kuma babbar barazana ga zaman lafiya da zamantakewar mu a wannan kasa.

Wadannan munanan rikice-rikice sai kara yaduwa su ke yi a fadin kasar nan. Don haka ya kamata dukkan mu mu tashi tsaye mu yi tufkar hanci.”

Daga nan sai ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su fito da yadda gwamnati, kungiyoyi, kafafen yada labarai har ma da sarakunan gargajiya za su taka rawar magance wannan matsalar.

Share.

game da Author