Sarkin Musulmai Sa’ad Abubakar III ya yi tir da jita-jitan da ake ta yadawa akan cewa alluran rigakafin cutar shan inna da wasu cututtuka da ke kashe yara kanana da gwamnati ke badawa gurbatattune.
Ya fadi haka ne a taron sanin madafa don kawar da cutar shan inna karo na uku da aka yi a garin Lafia jihar Nasarawa ranar Talata.
Ya ce jita-jitan da ake ta yadawa kan alluran rigakafin wai ya na kashe wasu mutane ko kuma mabiyan wata addini bai haka bane.
Saboda hakan yake kira ga masu yada irin wannan mummunar jita-jita da su daina yin haka.
Sa’ad Abubakar ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya,shugabanin addini da sauran mutanen Najeriya da su taimaka wajen wayar da kan mutane kan mahimmancin yin alluran rigakafi.
Bayan haka gwamna Al-Makura ya mika godiyarsa ga mai martaba sultan Abubakar domin irin goyan bayan da yake badawa wajen kawar da cutar shan inna da sauran cututtuka a kasar nan.
Discussion about this post