BUHARI: ‘Ina mamakin yadda gwamnoni ke iya barci alhali sun ki biyan ma’aikata albashi’

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya fusata dangane yadda gwamnoni ke kasa biyan albashin ma’aikatan jihohin su, duk kuwa da irin makudan kudaden da Gwamnatin Tarayya ke dankara musu.

Buhari ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya karbi tawagar wasu gwamnoni da su ka ziyarce shi, a karkashin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya, Abdul’aziz Yari na Zamfara.

Shugaba Buhari ya ce musu a gaskiya ya kamata duk abin da su ke yi, to su rika tunawa da hakkin ma’aikatan jihohin su. Ya na mai tunatar da su cewa su sani fa wasu ma’aikatan fa mutu-kwakwai-rai-kwakwai su ke, domin albashin kawai su je jira.

“Ni fa ina mamakin yadda gwamna zai kwanta har ya iya sharar barci, alhali ga ma’aikatan jihar sa can su na jiran tsammanin biyan su albashi da hakkokin su da ya ki biya.

“Ina kuma mamakin yadda ma wadannan ma’aikata ke iya ciyar da iyalin su, su biya kudin haya da kudin makarantar ‘ya’yan su.” Inji Buhari.

Ya ci gaba da cewa tilas gwamnatin tarayya ta zauna da gwamnonin jihohi domin a maganace kin biya ko kasa biyan albashin ma’aiktan jihohin su da ba su iya yi.

“Allah ya sa ma bana an samu damina ta yi kyau, jama’a da dama sun yi noma, kuma gwamnati ta rage harajin shigo da kayan abinci daga waje. Amma ba don haka ba, ai da ma’aikata sun shiga cikin wahala.”

Da ya mike ya ke jawabi, Gwamnan Jihar Zamfara, Yari, ya bayyana wa shugaban kasa cewa yawancin jihohi sun tsinci kan su cikin tirka-tirkar dimbin bashin kudin da suka gada daga, wadanda gwamnonin da suka sauka su ka ciwo.

“Mu ma kan mu abin na damun mu, amma kuma lokacin da wasun mu da dama su ka hau, sun tarad da ma’aikatan jihohin su na bin jihohi dimbin bashin kudin albashi, fansho da garatuti na watanni da dama wadanda gwamnonin da ba su biya ba.”

Sauran gwamnonin da su ka kai ziyarar sun hada da na Bauchi, Jigawa, Kwara, Akwa Ibom da kuma mataimakin gwamnan Ebonyi.

Share.

game da Author

Comments are closed.