Ganin yadda Gangamin Taron jam’iyyar adawa ta kasa, PDP ke gabatowa nan da watan Disamba mai zuwa, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ja kunnen daukacin ‘yan PDP, musamman Babban Kwamitin Gudanarwar jam’iyyar, da su kiyaye da wadansu shawarwari da ya zayyana musu:
SHUGABANCIN JAM’IYYA:
Jonathan ya bada shawarar cewa a tabbatar da an zabi mutumin kwarai nagari ya kasance shi ne zai shugabanci jam’iyyar. Ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya karbi dan takarar shugabancin jam’iyyar, Raymond Dokpesi da ‘yan tawagar sa, a gidan Jonathan da ke Abuja, jiya Talata.
GUDUN SAKE TAFKA KUSKURE:
Ya ja hankalin kada a sake tafka kuskuren zaben baragurbin shugaban jam’iyya da kuma sakataren yada labarai na jam’iyya. Domin a cewar sa, su ne mukaman da su ka fi daukar hankali a kowace jam’iyya.
“Don haka mu a wannan karon mu na bukatar mutum mai karfin hali kuma mai kaifin bakin magana shi ne ya kamata ya zama shugaban jam’iyya.”
DAUKAR DARASI:
Jonathan ya ce: “Akwai mukamai biyu masu muhimmanci a jam’iyya, wadanda ba za mu yi sake mu sake yin irin kuskuren da mu ka yi a baya kan wadannan mukamai ba. Su ne mukaman shugaban jam’iyya da na sakataren yada labarai. Ni na fi kowa dandana kudar kuskuren da mu ka yi a baya.”
WANDA BAI JI BARI BA…
“Idan muka tafka kuskuren zaben mutanen da ba su dace ba, mu ka ba su mukaman shugaban jam’iyya da sakataren yada labarai na jam’iyya, to mun gama yawo.”
SAI WANDA KUDI BA SU RUFE MASA IDO:
“A wannan karo, mu jajirce mu zabi wanda ba shi da sanyin jiki, wanda idan ya ce a yi, to za a yi. Idan ya ce kada a yi, to ba za a yi ba. Ya kasance nagari wanda ba ya tsoron barazanar kowa. Sannan kuma wanda ba za a zo a bude masa ido da kudi ba domin a zabi dan takarar da bai cancanta ba.”
NAGARI NA KOWA:
“Idan mu ka zabi shugaba nagari, to akwai yiwuwar sake cin zabe fiye da idan aka zabi shugaba rubabi-rubabi. Mu na bukatar shugaban jam’iyya wanda zai hada kan ‘yan kwamiti na kasa baki daya kuma ya rika tuntubar ‘yan kwamiti na jiha domin a yi wa jam’iyya abin da ya fi dacewa a yi mata.”
SIRRIN LAKANIN:
“Sirrin lakanin shi ne domin idan 2019 ta zo, to za mu tunkari zabe da karfin mu, PDP za ta lashe mafi yawan kujerun majalisun jihohi da na tarayya. Sannan kuma za ta lashe zaben shugaban kasa.”
BUKATAR HADA KAI:
“Ya kasance an yi zaben shugabanni, ba dauki-dora aka yi ba. Kuma duk wanda aka kayar, to ya rungumi kaddara a matsayin sa na mai kishin jam’iyya.”
BA A BORI DA SANYIN JIKI:
“Ya kamata jam’iyyar PDP ta mike tsaye ta na nuna adawa sosai domin a rika ji da ganin jam’iyyar na cika-ido. Ta haka dimokradiyyar za ta kara karsashi. Amma ba cewa na yi a rika fitowa ana surutu barkatai kamar indararo ya gafce ba. Ba a san PDP da irin wannan ba, domin jam’iyya ce ta natsatstsu.”
“Fitowa mu na magana zai hana jam’iyya mai mulki ta rika yin karfa-karfa da babakere. Amma idan ana magana, to ba za ta rika yin abin da ta ga dama ba. Ai ko’ina a duniya ba a san jam’iyyar adawa da yin likimo ba.”
A karshe Jonathan ya yaba da irin namijin kokarin da Ahmed Makarfi ke yi a yanzu da ya ke shugabancin riko na jam’iyyar. Ya kuma jinjina wa Raymond Dokpesi ya na mai yi masa addu’ar samun nasara.
“Dokpesi mutum ne mai kishin jam’iyya kuma ya dade ya na yi mata hidima da kudin sa.” Inji Jonathan.