Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa tsohon gwamnan jihar Kaduna Balarabe Musa a murnan Cikan sa shekara 81 a duniya.
Buhari ya ce irin su Balarabe Musa mutane ne da ke da kima a idanuwar jama’a sannan mutum ne mai dattaku.
” Yau duk adawarka baza ka karyata irin kishi da son yi wa jama’a musamman talakawa aiki da Balarabe Musa ya ke da shi ba.”
” Balarabe Musa mutum ne da ba jihar Kaduna ba kawai a Kasa baki daya ana yaba masa saboda ra’ayin sa na son ci gaba da taimaka wa talakawa.
” Ina masa fatan Alheri da tsawon kwana mai albarka.
Discussion about this post