Kwamishinan kiwon Lafiya a jihar Kano ya sanar da cewa an sami rahoton wani da ake zargin yana dauke da cutar ‘Monkey Pox’ a karamar hukumar Bebeji, dake jihar Kano.
Kwaishinan ya ce tuni an killace shi sannan an aika da jini sa Abuja domin sanin ainihin bayanai akan cutar da yake dauke da ita.
Ya ce ko da yake ana ganin kamar bakondauro ne amma amma duk da haka sai an dawo da sakamakon gwajin kafin a tabbatar da abin da yake dauke da shi sanna kuma an killace duk wadanda suka yi hudda da shi wannan mara lafiya su 60 ana duba su.
Discussion about this post