APC a jihar Jigawa ta yi babban Kamu

0

Jiga-jigan jam’iyyar APC sun yi cincirundo yau a filin Wasa dake garin Dutse domin tarban sanata Danladi Sankara da ya canza Sheka zuwa jam’iyyar APC daga PDP.

Gwamnan jihar Mohammed Badaru Wanda shine ya tarbi sanata Sankara ya ce jam’iyyar APC tayi babban Kamu a jihar.

” Yanzu dai PDP ta mutu murus a jihar Jigawa domin sanata Sankara na karamin Kamu bane.”

Sanata Lawali Shu’aibu Wanda shine ya wakilci shugaban jam’iyyar APC a wajen bukin ya jinjina wa gwamnan jihar da jam’iyyar APC musamman a jihar Jigawa da wannnan Kamu da tayi na sanata Danladi.

Share.

game da Author