Sama da kasha 85 bisa 100 na daliban makarantun jihar Barno sun ci jarabawar WAEC da NECO

0

Sama da kasha 80 na daliban da suka zauna jarabawar Kammala makarantan Sakandare na WAEC da NECO a jihar Barno sun ci jarabawarsu da fiye da Kiredit 5 wanda ya hada da Turanci da Lissafi.

Jami’I a hukumar WAEC mai suna Zakari Abdullahi ne ya sanar da haka a ziyara da jami’an hukumomin suka kai wa gwamnan jihar Kashim Shettima.

Kashi 87.6 ne cikin 100 suka ci jarabawar daga makarantun gwamnatin jihar da masu zaman kansu.

Share.

game da Author