KIRA GA SIFETO JANAR DIN ‘YAN SANDA: Kayi wa Kwankwaso gargadi kan magoya bayansa –Majalisar Kano

1

Majalisar Dokokin jihar Kano ta yi kira ga Sifeto janar din ‘Yan sanda da ya gargadi tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa magoya bayan sa fada kan tada da hankali a jihar.

Dan Majalisa Hamza Massu, wanda shine shugaban kwamitin tsaro na majalisar dokokin jihar da yake fadin haka yace dole ne ya sa majalisar ta yanke haka ganin irin tashin hankalin da ya faru a wajen bukin hawan sallah bana.

Yace bayan wannan abu da ya faru mazauna garin Kano suna kokawa da ayyukan magoya bayan Kwankwaso da ake kira ‘Kwankwasiyya.’

Share.

game da Author