Tsoffin ministocin PDP biyu sun bayyana ra’ayin su cewa zai yi wuya jam’iyyar PDP ta ci zaben 2019.
Ministocin da suka bayyana wannan shakku akan haka sun hada da tsohon minstan harkokin ‘yan sanda Adamu Waziri, da kuma tsohuwar ministar harkokin mata, Zainab Maina.
Sun bayyana haka ne a wurin taron bayyana aniyar takarar shugabancin jam’iyyar da Tunde Adeniran ya yi, a Cibiyar Taro ta Shehu ‘Yar’Adua,a Abuja.
Sun ce muddun su na so PDP ta sake cin zabe, to sai jam’iyyar ta tsaida mutane nagartattu wadanda ba su da wani gyambon da ba su so jama’a su gani a kwaurukan su.
Waziri ya yi kira ga jam’iyyar da kuma magoya bayan ta cewa abin sai fa an zage damtse, domin jam’iyya mai mulki ba za ta zura ido haka kawai a karbi mulki a hannun ta ba.
Ita kuwa Maina cewa ta yi, “hanyar zuwa 2019 ta na da matukar wahalar bi, domin za a ci kwakwa kuma akwai gajiya sosai.”
Don haka ta ce idan ana so a yi nasara, to idan taron jam’iyya na kasa ya zo, kada a sake a tilasta wa jama’a dan takarar da ba sa so.
Shi kuwa tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ibrahim Mantu, cewa ya yi yanzu shi sabon tuba ne, kuma ya roki jama’a su yafe masa kuma a mince da duk abin da ya furta.
Sai dai kuma ya ce sai da ya yi azumin kwanaki 30, inda Allah ya yi masa isharar cewa Adeniran ne zai zama shugaban PDP na kasa.
Za a yi taron PDP na kasa ne a ranar 9 Ga Disamba, 2017