NAZARI NA MUSAMMAN: BUHARI, Mai Rabon Ganin Badi

0

A yanayin yadda Shugaban Kasa ya koma hutun ganin likita a London inda ya shafa sama da kwanaki 100 a can, gaskiyar magana wasu ‘yan Najeriya da dama sun yi tunanin kowane idan ma ya dawo gida, to sake labkewa zai yi a fada, ba zai rika fita ba, sai ranar Juma’a kamar yadda ya rika yi, bayan dawowar sa daga ganin likita a karon farko da ya je Landan ya zauna.

An yi ta surutai, jita-jita, karairayi da soki-burutsu iri daban-daban dangane da halin da Shugaba Muhammadu Buhari ke ciki a Landan.

Hatta wadanda su ka rika zuwa duba shi daga baya, kowa ya dawo sai ka ji ya ce Buhari ya na bukatar addu’a. Dama kuwa masoyan sa kama daga Musulmi zuwa Kiristoci,sun jajirce da addu’o’i.

Masu adawa kuwa daga masu cewa ya yi bankwana da shugabanci, sai ‘yan gaje-gani, wanda su ka tsiri zanga-zanga a birnin Landan da kuma Abuja su na yekuwar ko dai Buhari ya dawo, ko kuma ya sauka kawai.

Dawowar da ya yi ba zato ba tsammani ta bai wa ‘yan Najeriya da dama mamaki. A hakan ma, tunanin wasu shi ne ya dawo ne kawai saboda matsin-lambar masu zanga-zanga, amma bai gama murmurewa ba.

Sun sake kafa hujja da wannan ra’ayi ko dalili na su, ganin yadda Fadar Shugaban Kasa ta bayar da sanarwa cewa beraye sun gurgure wasu kayayyaki a ofishin Buhari, wanda ya kasance a rufe, tun bayan tafiyar sa Landan. Don haka daga gida zai rika aiki kafin a dauki lokacin gyara.

Sai dai kuma babban abin mamaki shi ne yadda Buhari ya bai wa kowa mamaki, da bai labke a kan gado ba, sai ya shiga aiki gadan-gadan.

Kadan daga ayyukan da ya yi bayan dawowar sa, sun hada da:

1 – Karbar rahoton kwamitin binciken zargin harkallar kwangilar datse ciyawa da ake yi wa Sakataren Gwamnatin Tarayya, wanda aka dakatar.

Sai kuma karbar sakamakon binciken harkallar tulin kudin da aka kama a wani gida a Legas, wanda binciken ya shafi Daraktan Jami’an Tsaro na Leken Asiri.

2 – Buhari ya ci gaba da fitowa karbar manyan baki daga kasashen waje kuma ya karbi shugabannin kasashe.

3 – Tafiyar sa Daura domin hutun Babbar Sallah, shi ma wani abu ne da ke nuna cewa lallai ya samu sauki. Domin shagalin bikin Sallah abu ne na cudanya da jama’a masu dimbin ya wa da za su rika kawo ziyarar gaisuwa.

5 – Zanga-zangar kungiyoyin kwadago, malaman jami’o’i, ma’aikatan jami’o’i da kuma malaman asibiti ba ta girgiza shi har ya sake bukatar ganin likita ba.

6 – Babbar rawar da Buhari ya taka bayan dawowar sa, ita ce murkushe ‘yan taratsin IPOB, masu so su kafa Biafra. An shafe shekara biyu shugaban kungiyar Nnamdi Kanu na barazanar yamutsa Najeriya domin ta watse, kowa ya kama gaban sa. Shi kan sa Buhari ya sha zagi na cin mutunci daga bakin Nnamdi Kanu.

Amma sai ga shi an wayi gari gogarman tsagerun, Nnamdi Kanu, ya arce. ba wanda ya san inda ya ke. Sannan kuma kafin Buhari ya gwada musu kwanji, IPOB sun bi ilahirin Yankin Jihohin Kudu maso Gabas sun baibaye ko’ina da tutar Biafra.

A yau babu Nnamdi Kanu, babu tutocin su, kuma babu sauran wani tsagera mai yawo kan titi ya na hauragiya. Su kan su sojojin baka da ‘yan taratsin Biafra a Facebook da sauran kafafe na soshiyal midiya, sun yi tsit. Wadanda ke alakanta shafukan su na Twitter, Instagram, WhatsApp da Facebook su na lika tutar Biafra, duk sun cire.

7 – Buhari ya yi ‘yan tafiye-tafiye a cikin gida, ciki kuwa har da zuwa kaddamarwa ko bude kamfanin sarrafa abincin kaji da na dabbobi a Kaduna.

8 – Wata babbar nasara kuma ita ce halartar da Shugaba Buhari ya yi a taron Majalisar Dinkin Duniya, a birnin New York na Amurka.

A wurin taron, karsashi, tasiri da kimar Buhari ta karu. Sannan kuma ya yi jawabin da dimbin masoyan sa ke ganin alama ce ta kankaro Najeriya da kuma Afrika a idon duniya.

Jawabin Buhari a wurin ya kara wa jama’a kwarin-guiwar cewa to tsoho fa dai ashe ya sauka da kwari. Idan aka kwatanta da jawabin sa bayan dawowa daga Landan, su kan su masu adawa sun san jiki dai ya kara murmurewa.

9 – Buhari ya yi namijin kokarin ganin ya biya ma’aikatan hukumar jiragen sama ta Nijeriya hakkin da su ke bi sama da shekara goma, kudin da sun zarce bilyan 200, wadanda gwamnatocin baya su ka gaza bilyan su.

10 – Zare idanun da Buhari ya yi wa gwamnoni masu taurin biyan ma’aikata albashi da sauran kudaden su, ya nuna cewa Shugaba Buhari da karfin sa ya dawo.

11 – Ci gaba da damke wadanda ake zargi da wawure dukikar kasar nan, ya tabbatar da cewa shugaban ba da wasa ya ke yi ba a jawabin sa bayan dawowar sa, inda ya ce ba zai sassauta ba daga himmar sa ta taka ruwan cikin duk wanda ya ci buzun Najeriya, domin ya wo aman gashi.

Tambaya a nan ita ce, me Shugaba Buhari zai maida hankali a kai, a cikin jawabin sa na gobe Lahadi, 1 Ga Oktoba, ranar murnar tunawa da samun ‘yanci?

Share.

game da Author