A ranar juma’a ne hukumar NEMA ta raba wa ‘yan gudun hijiran sansanonin jihar Taraba 10,433 kayayakin abinci domin tallafa musu a mazaunin su.
Shugaban hukumar Sanusi Ado ya sanar da hakan a sansanin Mutum Biyu dake karamar hukumar Gassol inda ya kara da cewa sakamakon cika alkawarin da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya dauka a watan Yuni a Maiduguri na tallafawa ‘yan gudun hijiran jihar Taraba ya sa suka ga haka.
Sanusi Ado ya ce su da kansu suke rarraba abincin giga-gida a sansanin saboda gujewa masu sama da fadi da kayayyakin.