Dalilan da ya sa kowani ni mai shirya fim ke sha’awar in yi masa editin din fim dinsa – Aminu Mu’azu

0

Fitaccen mai hada fim wato editin a farfajiyar fina-finan Hausa Aminu Mu’azu ya sanar wa PREMIUM TIMES cewa mai da hankali da kaunar hada hotuna ne ya sa shi samun nasara akan sana’arsa.

PT: Furodusosi da masu shirya fina-finan suna rubibin ka yi musu editin, Menene sirrin ka?

Aminu: Bani da wani sirri illa kaunar sana’a ta. Ina maida hankali wajen ganin na yi wani abu da ban taba yi ba domin in kara wa fim din kyau a duk lokacin da nake editin.

PT: An ce ka fara Darektin, shin haka ne?

Aminu: Haka ne domin nine nayi darektin fim din ‘ AL’UMMA NA’.

PT: Shin za ka ajiye aikin editin kenan ka fuskanci darektin?

Aminu: Inaa, ay editin yana jini na ne, ba zan iya barinsa ba. Darektin wani sana’a ce da bam da na ke so in kara a cikin jerin abubuwan da nake koya da wadanda na iya.

Duk wani edita ba ya iya bari sai dai ya kara wata sana’ar akan ta. Saboda haka ba zan iya bari ba domin yana jini na ne.

PT: Shin kana da yaran da ke karkashinka zuwa yanzu?

Aminu: Na yaye yara sama da 10 wanda yanzu suna cin gashin kansu ne. Sannan akwai wasu yanzu da suke karkashina ina koyar da su.

PT: Bayan yaran da kake koyarwa, Menene kuma kamfanin ka na Media Suite suke yi ko shirin yi nan gaba?

Aminu: Yanzu mun bude shafi a YouTube domin saka bidiyoyin mu a shafin. Bayan haka kuma muna shirin bude wajen koyarwa mai kama da makaranta domin matasa da suke so su zama masu hada bidiyoyi wato editoci Zamu koyar dasu sannan mu basu shaidar iya aiki bayan sun kammala. Hakan zai taimaka wajen samarwa matasa aikin yi da zasu iya rike kansu.

Ni kaiwa ban zauna haka ba domin kullum ina hanyar karo basira ce na yadda zan inganta aiki na. Sannan ina biyan kudade masu yawa don karo ilimi a harka sana’a ta. Bayan haka, nakan yi karatu ta shafuna a yanar gizo don koyon sarrafa bidiyoyi da hotuna irin na zamani don iya taka rawar gani a sana’ar editin da karawa fina finan mu na Kannywood kima a idanuwar mutanen duniya.

PT: Wani fim ne ka yi editin da ya yi matukar birge ka?

Aminu: Ay ni duk fim din da nayi editin ina alfahari da shi. Saboda haka babu wanda ya fi mini. Duk daya ne.

PT: Menene Burin ka a sana’arsa?

Aminu: Buri na shine ace yau na yi editin fim din Kannywood yayi kama da ‘Transformers’ da irin su ‘Mummy’.

Kuma ina hanya domin na dukufa sai na kai wannan wurin duk da cewa a haka ma gogan naka ba sauki. ( Dariya).

PT: Mun gode Aminu

Aminu: Na gode PREMIUM TIMES.

Share.

game da Author