Farfesa Sagay, Mashawarcin Buhari dan tasha ne, cewar APC

0

Jam’iyyar APC mai mulki ta kira Mashawarcin kuma Shugaban Kwamitin Shugaba Buhari kan Harkokin Hana Cin Hanci, Farfesa Itse Sagay a matsayin dan tasha, wanda ba ya ganin girman hatta shi kan sa Shugaban Kasa din.

Sun maida masa wannan kakkausan martani ne biyo bayan wata tattaunawa mai zafin gaske da aka yi da shi a ranar Lahadi, 24 Ga Satumba, a cikin jaridar ‘The Nation’, inda ya kira shugabannin Jam’iyyar APC a matsayin marasa kima, dattaku da rashin alkibla.

A cikin wata takarda da Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya sa wa hannu a yau Litinin, APC ta bayyana Sagay a matsayin ‘’rudaddar giwar da ba a iya sarrafa ta.’’

“A cikin wannan gwamnati idan ana neman wanda babu ruwan sa da ganin mutuncin kowa sai mutuncin kan sa, wanda bai san hikimar yi wa harshen sa linzami ba, wanda ya ke jin ba mai iya tankwara shi, wanda ke jin ya fi karfin kowa da kowace hukuma, to wannan mutumin shi ne Farfesa Itse Sagay.”

Shi ma Sagay ya kira shugabannin da sunan ’yan bankaura wadanda ba su san komai ba, sai fa kara lalata jam’iyya. Haka ya bayyana su a cikin hirar sa da ‘The Nation’.

Da aka tambayi Sagay ganin yadda ya ke yawan magana, ko idan Shugaba Buhari ya ce ya yi shiru haka nan zai yi kuwa? Sai ya ce kwarai zai iya yin shiru mana tunda Buhari shugaban sa ne. Amma kuma ya ce sai dai akwai yanayin da idan aka kai shi bango, to ba fa zai iya yin shiru ya bi umarnin wani ba, sai dai ya bi umarnin zuciyar sa. A cewar sa, akwai yanayin da kowane dan Adam ke bukatar ’yancin kan sa.

“Saboda tsananin girman kai ta Sagay, ya manta cewa idan ka na yin zagi a cikin kasuwar APC, to ko ba ka kira suna ba fa, ai har da Shugaban Kasa ka hada ka zaga kenan.

“Idan Sagay dan mutunci ne, ai bai kamata ya manta da mutumin da ya tsamo shi daga cikin rami, ya ajiye shi a kan tsandauri, ya mutunta shi a cikin gwamnati ba, har ya ke irin dagewar da yake yi a yanzu.

“Maimakon ya rika mika shawarwarin sa ga Shugaban Kasa, sai ya maida kai wajen yaga wa kowa rigar mutunci kawai.

“To mu na so mu shaida wa Sagay cewa duk ma wani mai rike da mukami a wannan gwamnatin, albarkacin APC ya ke ci, domin ya samu mukamin ne sanadiyyar nasarar kafa mulkin da APC in da ya ke zagi ta yi.

Bolaji Abdullahi ya tunatar da Sagay cewa bai yiwuwa mutum ya ce ya na son dan mangwaro, sannan kuma ya ce ba ya kaunar bishiyar mangwaro.

Share.

game da Author