Dokar hana mata cire cikin da basa so hatsari ne ga rayukansu

0

Kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO da hukumar gudanar da bincike akan matsalolin haihuwa dake kasar Amurka mai suna ‘Guttmacher Institute’ sun gudanar da bincike akan illar da dokar hana cire ciki ke yi wa mata musamman a kasashen da ke ci gaba.

Saboda gudun haka, matan sukan je wajen wasu likitocin da basu kware ba domin cire cikin a boye kuma sau da yawa za ka ga hakan ya sa suna ta mutuwa.

Binciken ya nuna cewa tsakanin shekarun 2010 da 2014 mata miliyan 25.5 a duniya sun cire ciki ta hanyar da bai dace ba sannan kashi 97 bisa 100 daga ciki an yi su ne a kasashen da ke ci gaba kamar Afrika, Asia da Latin America.

” Hakan ya nuna cewa dokar ba wai tana hana mata zubar da ciki bane sai dai ta saka su cikin mummunar matsala.”

Kungiyar WHO da hukumar Guttmacher sun bada misalin kasa Najeriya inda aka hana mata cire ciki sai dai idan cikin zai ya zamo da matsala a cikinta ko kuma ya kai ta ga rasa rayuwarta.

“Hakan ya sa mata da dama zuwa cire ciki wurin likitocin da ba su kware ba a aikin sannan bayan an gama su sami matsalar zubar jini wanda daga baya su mutu.”

Wata jami’ar kungiyar WHO Bela Ganatra ta yi kira ga kasashen da suka kafa dokar hana cire ciki da su samar da dabarun bada tazaran iyali ga iyalansu sannan su wayar da kan matan da amincewa da dabarun tazaran iyali sannan kuma su kafa dokar da zai bar mata cire ciki.

Ta ce hakan zai taimaka wajen ceto rayuwar mata domin kasan za ta sami likitocin da suka kaware a aikin.

Share.

game da Author