TAMBAYA: Shin ana sa kaya a Aljanna ko kuwa yadda a ka tashi haka za a ci gaba da zama?

0

TAMBAYA: Malam shin ana sa kaya a Aljanna ko kuwa yadda a ka tashi haka za a ci gaba da zama?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Ya kai dan-uwa, Allah ya kara maka Imani, lalle ana sa kaya a Aljanna, kayan ‘yan Aljanna masu kyau ne, babu wani kaya da yayi kyansa. Wata rana an kawo ma Manzon Allah (SAW) wani yadi na Alharini mai tsananin kyau, sai kyansa da taushin sa yayi matukar burge sahabbai, sukayi ta mamakin kyansa, sai Manzo Allah (SAW) yace: baikai kyan hankicin Sa’ad dan Mu’azu ba na Aljanna. Tufafin ‘yan Aljanna musu kyau ne, basa tsufa, basa datti, basa lalacewa. Kuma masu kyalli da sheki ne, sannan sabuntasu karuwa take yi, kamar sukan su ‘yan Aljannar.

Al-Kur’ani yayi bayanin haka a cikin surori kamar Al-Hajj:23, Al-Insan: 12 : 21, Fadir: 33, Al-Kahaf:31, da sauran Hadisai da yawa.

‘Yan Aljanna suna sanya sutura ta alfarma, suna ado da kwalliya a cikin Aljanna da kaya, zinare, azurfa , lu’u-lu’u da dukkan sauran kayan ado wanda zuciya bata daba tunaninsu ba, balle kuma ido ya gansu.

Tufafin ‘yan Aljanna na Alharinine mai tsananin kwyau da kanshi, kayan ‘yan Aljanna kala-kala ne, masu launi daban – daban kuma akwai laulin kore dagacikin launin kayan ‘yan Aljanna.

Ya Allah! Muna rokon ka da sunayen ka kyawawa, ka azurtamu da Aljannar ka da Ni’imar ta, kuma ka tsaremu daga wutarka da Azabarta. Amin Ya

Share.

game da Author